in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin Chadi sun harbe dakarun kungiyar Boko Haram 63 har lahira
2019-04-16 10:05:42 cri
Bisa labarin da kafofin watsa labaru na kasar Chadi suka bayar a ranar 15 ga wata, an ce, sojojin kasar sun harbe dakarun kungiyar Boko Haram 63 har lahira a wani wurin gadi na aikin soja dake dab da tabkin Chadi a daren ranar 14 zuwa sassafen ranar 15 ga wannan wata.

Labarin ya tsamo sanarwar da bangaren soja na kasar Chadi ya bayar a ranar 15 ga wata cewa, dakarun sun kai hari da daddare. Sojojin kasar Chadi 7 sun mutu a sakamakon aikin soja da aka yi na martani ga harin, kana sojoji fiye da 10 sun ji rauni.

Wannan ne karo na biyu da aka yi musayar wuta mai tsanani a tsakanin sojojin kasar Chadi da kungiyar Boko Haram a cikin wata guda. Bisa labarin da kafofin watsa labaru suka bayar, sabon hafsan hafsoshin sojojin kasar Chadi Tahir Erda ya bayyana a yayin da yake yin rangadin aiki a sansanin yaki da ta'addanci a kwanakin baya cewa, ana bukatar daukar sabbin matakai don yaki da kungiyar Boko Haram. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China