in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
FAO ta yi gargadi game da matsalar fari dake addabar yankunan tafkin Chadi
2017-04-12 20:36:11 cri

Hukumar abinci da aikin gona ta MDD FAO, ta bayyana karuwar zafi, da matsaloli masu nasaba da tashe tashen hankula, tare da amfani da tsaffin dabarun noma, a matsayin dalilan dake jefa kasashe 4 dake yankin tafkin Chadi cikin yanayi na fari.

Babban Daraktan hukumar ta FAO Jose Graziano da Silva, wanda ya kammala wata ziyara ta kwanaki 3 a yankin ne ya bayyana hakan ga manema labarai a ranar Talata.

Ya ce tafkin Chadi na samar da ruwan sha, kuma makiyaye ce ga tarin dabbobin dake kasashen kewayen yankin. Kaza lika ruwan sa na taimakawa wajen noman rani, da sana'ar su a sassan kasashen Kamaru, da Chadi, da Nijar da kuma Najeriya.

Mr. Graziano da Silva, ya kara da cewa samar da managartan irin shuka a daidai watannin Mayu da Yuni, lokacin da ake shiga yanayi na damuna, zai taimakawa manoman yankin marasa karfi, wajen noma isasshen abinci da zai tallafi rayuwar su.

To sai dai kuma jami'in na hukumar FAO ya nuna damuwa, game da yadda ake ci gaba da fuskantar jinkiri, wajen samun kudaden da aka alkawarta bayarwa domin samar da wannan taimako. Ya ce cikin dalar Amurka miliyan 62 da aka alkawarta tarawa a bara, yanzu haka dala miliyan 10 ne kacal suka samu.

Mr. Graziano da Silva, ya ce idan har aka gaza samar da tallafin da ya wajaba, al'ummun wannan yankuna na tafkin Chadi, da yawan su ya kai 50,000 na iya fuskantar matsalar fari mai tsanani.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China