in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Samar da yankin masana'antu a kasashen ketare ya haifar da manyan nasarori in ji wani rahoto
2019-03-18 10:22:21 cri
Wani rahoton baya bayan nan ya ce matakin da kasar Sin ta aiwatar, na kafa yankunan masana'antu a kasashen ketare, ya zaburar da burin da ake da shi na bunkasa hadin gwiwa, karkashin shawarar ziri daya da hanya daya.

Rahoton na hukumar samar da bayanai game da tattalin arzikin kasar Sin, ya ce kamfanonin Sin sun ba da gudummawa matuka, wajen gina yankunan hadin gwiwa a fannin raya tattalin arziki da cinikayya, a kasashe daban daban dake cikin shawarar ziri daya da hanya daya.

Rahoton ya ambaci yankin masana'antu na Sin da Belarus, da na Sin da Malaysia, a matsayin "muhimman yankuna biyu", baya ga yankin masana'antu na Sin da Masar na Suez, da ma yankin hadin gwiwar cinikayya dake tsakanin sassan biyu, wadanda suka zamo zakaran gwajin dafi a fannin bunkasar hadin gwiwar Sin da sauran kasashe da suka karbi shawarar ziri daya da hanya daya.

Kamfanonin kasar Sin dai sun zuba jarin da yawan sa ya kai dalar Amurka biliyan 15.64 a sassan da ba na hada hadar kudade ba, karkashin manufar ziri daya da hanya daya a shekarar 2018, adadin da ya karu da kaso kusan 8.9 bisa dari a shekara guda, wanda kuma ya kai kaso 13 bisa dari, na adadin jarin da suka zuba a irin wannan sassa a shekarar.

Rahoton ya ce manufar kafa yankunan masana'antu a kasashen ketare, ta yi tasiri a fannin bunkasa kasuwanni, da samar da muhimman abubuwa na ci gaba, da hajoji da kasuwanni ke bukata.

Kasar Sin ta gina sassan yankunan hadin gwiwa a kasashen waje, a fannin raya ayyukan noma musamman a yankunan tsakiyar nahiyar Asiya, da kudancin nahiyar, da nahiyar Afirka, domin tallafawa manoman yankin samun karin yabanya, da riba mai tarin yawa.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China