in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ba ta taba tilastawa wani bin shawarar "ziri daya da hanya daya" ba
2019-02-13 10:37:10 cri

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Madam Hua Chunying ta bayyana jiya Talata cewar, yayin da ake kokarin raya ayyuka bisa shawarar "ziri daya da hanya daya", kasar Sin ba ta taba tilastawa wani wajen shiga ciki ba, haka kuma ba ta taba gindaya wani irin sharadi da zai yi wahalar amincewa ba. Tana mai cewa, ana gudanar da ko wane aiki ne bisa shawarari tsakanin bangarori daban daban cikin adalci.

Madam Hua ta yi wannan furuci ne a yayin taron manema labarai, inda ta kara da cewa, kawo yanzu dai, kasashe da kungiyoyin duniya fiye da 150 sun sa hannu kan yarjeniyoyin hadin kai tare da kasar Sin bisa shawarar "ziri daya da hanya daya", kuma dimbin ayyukan da abin ya shafa sun riga sun samu kyawawan sakamako. Lamarin da ya kara kwarin gwiwar kasashen da shawarar ta shafa wajen bukasar tattalin arziki da zamantakewar al'ummarsu. Samun bunkasuwa gaba daya bisa yin shawarari tare don moriyar juna, babbar ka'ida ce wajen raya shawarar "Ziri daya da hanya daya". Yayin da kasar Sin ke ingiza shawarar tare da kasashen da abin ya shafa, ko da yaushe ta kan bi ka'idojin zaman daidai wa daida, da bude kofa ba tare da boye komai ba, da ma bin ka'idojin kasuwanci na kasa da kasa. (Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China