in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin za ta kaucewa danawa kasashen dake cikin shawarar "Ziri Daya da Hanya Daya" tarkon bashi
2019-04-08 10:51:30 cri
Jakadan kasar Sin a tattaunawar harkokin hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen Larabawa na ma'aikatar harkokin wajen kasar, Li Chengwen, ya yi watsi da sukar da ake cewa, shawarar "Ziri Daya da Hanya Daya", za ta dana tarkon bashi ga kasashen da suka amince da ita.

Li Chengwen, ya bayyana haka ne a jiya, yayin wani zama a zagaye na 2 na taron tattalin arzikin duniya kan yankin gabas ta tsakiya da yankin arewacin Afrika na 2019 da ya gudana a yankin mataccen teku na kasar Jordan.

Jakadan ya ce manufar shawarar "Ziri Daya da Hanya Daya" ita ce, bunkasa tattalin arzikin kasa. Amma ba fadada karfi da ikon kasar Sin akan sauran sassan duniya ba.

A cewar Sakataren cinikayya na majalisar dokokin Pakistan, Shandana Gulzar Khan, idan kasa ta kiyaye bukatunta, to babu yadda za ta kalli kasar Sin a matsayin abokiyar hulda mara gaskiya. Ya ce a Pakistan, babbar kasa cikin shawarar, huldar tattalin arziki tsakaninta da kasar Sin ya samar da dubban ayyukan yi tare da farfado da tattalin arzikin yankin da take baki daya.

Jakadan na kasar Sin, ya yi furucin ne a matsayin martani ga sukar da wasu daga Turai da Amurka ke yi, gabanin taro na 2 na hadin gwiwar kasa da kasa karkashin shawarar, wadda kasar Sin za ta karbi bakuncinsa a wannan watan a birnin Beijing. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China