in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An gudanar da gwajin bikin baje kolin lambunan shakatawa na Beijing
2019-04-15 09:52:31 cri

An gudanar da gwajin bude wurin da za a yi bikin baje kolin lambunan shakatawa na kasa da kasa na Beijing na 2019 a ranar Asabar, don gwada yadda bikin zai karbi mutane.

Kimanin mutane 30,000, galibi mazauna yankin Yanqing dake arewacin birnin Beijing da ya karbi bakuncin bikin, su ne rukuni na farko da suka kai ziyara wajen mai fadin kadada 503, a kasan wani bangare na babbar ganuwar kasar Sin.

Bikin da za a fara a ranar 29 ga wannan watan, wanda zai shafe kwanaki 162, na da nufin burge baki kimanin miliyan 16 daga ciki da wajen kasar Sin, inda zai gabatar da tarin tsirrai da furanni da rumfuna masu kayatarwa da kuma dabarun raya muhalli ta hanyar shuke-shuke.

Sama da kasashe da kungiyoyin kasa da kasa 110 da sama da kungiyoyi 120 da ba na gwamnati ba, sun tabbatar za su halarci bikin, wanda zai zama irin bikin mafi samun masu ziyara a tarihi.

A cewar mashirya bikin, rukunin masu bada hidima yayin gwajin da aka yi a ranar Asabar, ya kunshi ma'aikata 4,000, wadanda suka yi aikin karbar da jagorantar baki da kuma ayyukan tabbatar da tsaro. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China