in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin: Ana share fagen taron baje-kolin kayayyakin da ake shigo da su na duniya karo na 2
2019-04-13 16:54:18 cri

Wakilinmu ya ruwaito cewa, share fagen taron baje-kolin kayayyakin da ake shigowa da su na duniya karo na 2, ya kan-kama yadda ya kamata, inda kamfanoni da dama za su halarta.

Liu Fuxue, mataimakin shugaban hukumar kula da taron baje-kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin na duniya, ya ce, za a kara girman taron da za a bude a watan Nuwamban bana, inda fadin wuraren nune-nune zai karu da murabba'in mita dubu 30, bisa na taron na farko, don haka, fadin wuraren nune-nunen zai kai murabba'in mita dubu 300 baki daya a wannan karon. Kana, za a ci gaba da kara azama kan yin kirkire-kirkire, inda wasu kamfanoni za su halarci taron da sabbin kayayyakinsu. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China