in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen duniya sun nuna karfin zuciya kan tattalin arzikin kasar Sin
2019-04-11 19:12:31 cri

Yau Alhamis, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang, ya bayyana a nan Beijing cewa, kara hasashe kan bunkasar tattalin arzikin kasar Sin, da asusun ba da lamuni na kasa da kasa wato IMF ya yi, ya nuna cewa, kasashen duniya sun nuna karfin zuciya kan yadda kasar Sin take tabbatar da saurin bunkasuwar tattalin arzikinta.

A ranar 9 ga wata asusun IMF ya kara hasashen da ya yi kan bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin zuwa kashi 6.3 cikin dari a shekarar 2019 a cikin sabon rahotonsa, wanda ya karu da kashi 0.1 cikin dari bisa yadda ya yi hasashe a watan Janairun bana, yayin da ya rage hasashen da ya yi kan bunkasuwar tattalin arzikin duniya zuwa kashi 3.3 cikin dari a shekarar 2019, amma hasashen ya nuna a watan Janairun shi ne kashi 3.5 cikin dari. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China