Liu Fuxue, mataimakin shugaban hukumar kula da bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin ya bayyana a yau Jumma'a, cewar za a kara girman bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin karo na biyu, wanda fadin filin nune-nunan kayayyakin kamfanoni zai kai murabba'in mita dubu 300, karin murabba'in mita dubu 30 bisa na bara. Haka kuma za a yi kokarin gayyato karin kasashe da yankuna da ma kamfanoni domin su shiga bikin, ta yadda za a ba su damar shiga kasuwar Sin. Ban da wannan kuma, za a kara karfin jawo hankalin kamfanoni masu zaman kansu da kanana da matsakaitan masana'antu.
Ana sa ran za a gudanar da bikin a karo na biyu a birnin Shanghai daga ranar 5 zuwa 10 ga watan Nuwamban bana.(Kande Gao)