in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a gayyaci karin kamfanoni masu zaman kansu su halarci CIIE karo na 2
2019-04-04 19:31:49 cri

Yau kakakin watsa labarai na ma'aikatar kasuwancin kasar Sin Gao Feng ya bayyana a nan Beijing cewa, kawo yanzu adadin kamfanonin da suka gabatar da bukatar halartar CIIE wato bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin karo na 2 ya kai sama da 1800, kasar Sin za ta gayyaci karin kamfanoni masu zaman kansu da kanana da matsakaitan kamfanoni da su halarci bikin na CIIE, haka kuma za ta gayyaci karin 'yan kasuwan kasashen waje da su ma su halarci bikin domin tattauna yadda za su sayar da kayayyakinsu.

Kakakin ya kara da cewa, yanzu haka ana kokarin gudanar da aikin share fagen bikin karo na 2, ma'aikatar kasuwancin kasar za ta ci gaba da ingiza aikin, tare kuma da shirya dandalin tattalin arzikin kasa da kasa na Hongqiao na birnin Shanghai, ta yadda za a tabbatar da gudanar CIIE karo na 2 cikin nasara(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China