Ndlovu ya bayyana cewa, an yi maraba sosai ga tawagar kasar Zimbabwe da ta halarci bikin CIIE na Shanghai, yana mai godiyawa mashirya bikin. A ganinsa, bikin CIIE ya shaida imanin Sin na bude kofa ga kasashen waje, yana mai cewa, a karkashin yanayin tsananta rikicin ciniki na duniya da ra'ayin ba da kariya ga cinikayya, bikin CIIE ya shaida wa duniya manufar Sin ta bude kofa ga kasashen waje, don haka bikin CIIE muhimmin biki ne.
Game da yanayin fitar da kayayyaki daga kasar Zimbabwe zuwa kasar Sin kuwa, Ndlovu ya bayyana cewa, ko da an gudanar da tattaunawa yayin bikin CIIE, ana bukatar kamfanonin kasar Zimbabwe su kara yin kokarin fadada kasuwarsu a kasar Sin. (Zainab)