Jaridar ta ce an tura manyan jami'ai karkashin jagorancin Liu Fuxue, mataimakin shugaban hukumar kula da CIIE, zuwa kasashen Australia da New Zealand, domin gayyato 'yan kasuwar wuraren.
Liu Fuxue, ya ce tun daga watan Yulin bana aka fara rejistar baje kolin na badi, kuma akwai bukatar wadanda ke sha'awar zuwa su yi rejista kafin 30 ga watan Afrilun 2019.
Liu ya kara da cewa, kimanin kamfanoni 100 ne suka rattaba hannu kan kwangiloli tsakaninsu da hukumar kula da CIIE, inda kuma ake ci gaba da tattaunawa game da wasu karin kwangilolin. (Fa'iza Mustapha)