in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kudaden cinikayyar da za a yi sakamakon bikin baje koli na CIIE za su kai dala biliyan 57.83
2018-11-10 20:53:16 cri
Mashirya bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su nan kasar Sin irin sa na farko da ya kammala yau Asabar a birnin shanghai na kasar Sin, sun ce kudaden cinikayyar da za a yi cikin shekara guda mai zuwa, sakamakon yarjeniyoyin cinikayya da aka kulla yayin baje kolin na CIIE, za su kai dalar Amurka biliyan 57.83.

Da yake tabbatar da hakan, yayin wani taron manema labarai da ya gudana, mataimakin daraktan hukumar shirya baje kolin Sun Chenghai, ya ce adadin kasashe 172 ne suka halarci bikin na yini shida, baya ga yankuna daban daban, da wakilan kungiyoyin kasa da kasa, tare da masu kamfanoni ko sana'o'i 3,600. Kaza lika bikin baje kolin ya jawo masu sayayya na gida da na waje sama da 400,000.

Yarjejeniyoyi na hada hadar kayayyakin na'urori masu kwakwalwa su ne kan gaba, inda darajar cinikayyar su za ta kai dala biliyan 16.46, sai kuma kayayyakin abinci da na amfanin gona, wadanda za su kai dala biliyan 12.68, kana na kayan kirar motoci za su kai dala biliyan 11.99.

Sauran sun hada da na kayayyakin kiwon lafiya na dala biliyan 5.76, da kayan latironi na dala biliyan 4.33, da na kayan amfanin yau da kullum na dala biliyan 3.37, yayin da na ayyukan hidima za su kai dala biliyan 3.24. A daya hannun kuma, hasashen cinikayyar da za a yi tsakanin kasashen da shawarar ziri daya da hanya daya ta shafa, zai kai na dalar Amurka biliyan 4.72. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China