in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wasu abubuwa "na farko" da aka samu a ziyarar farko da shugaba Xi Jinping ya kai a bana
2019-03-28 11:02:46 cri

Shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya gudanar da ziyarar aiki a kasashen Italiya, Monaco da Faransa bisa gayyatar da kasashen 3 suka yi masa daga ranar 21 zuwa 26 ga wata. Ziyarar da ya kai nahiyar Turai, ita ce ziyara ta farko da shugaban ya gudanar a bana. A lokacin ziyara tasa, shugaba Xi ya ga abubuwa da dama wadanda suka abku a karo na farko, lamarin da ya nuna cewa, kasashen Sin da Turai suna kokarin kulla huldar abota a tsakaninsu a kokarin tabbatar da zaman lafiya, bunkasuwa, yin gyare-gyare da wayin kai.

Kasar Italiya ita ce ta farko a cikin kasashe mambobin kungiyar G7, wadda ta shiga shawarar "Ziri Daya da Hanya Daya".

Haka kuma, wannan shi ne Karo na farko da shugaban kasar Sin ya ziyarci kasar Monaco.

Kasar Faransa ta bai wa shugaban kasar Sin kyautar wani littafin Faransanci, wanda aka wallafa a shekarar 1688 dangane da kalaman Confucius da mabiyansa a karon farko.

Sin da Faransa sun shirya taron dandalin tattaunawa kan tafiyar da harkokin duniya karo na farko, sa'an nan shugaba Xi ya yi shawarwari da takwaransa na Faransa, shugabar gwamnatin kasar Jamus, da shugaban hukumar zartarwar kungiyar EU.(Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China