An samu karuwar kasa da 0.3 ne a makamancin lokacin bara, kamar yadda ma'aikatar kula da masana'antu da fasahar sadarwa ta kasar Sin ta sanar.
An samu bunkasuwar kudaden shiga a fannonin babbar cibiyar adadin bayanai da ayyukan bada hidima ta intanet, da cinikayyar fasahohin zamani da kashi 16.8 bisa 100 tsakanin watan Janairu zuwa Fabrairu. Cinikayyar manhajojin zamani ya karu da kashi 11.1 bisa 100 idan an kwatanta da makamancin lokacin shekarar 2018.
Ribar da aka damu a cinikin manhajojin na'urorin zamani da ayyukan fasahar sadarwa na zamani IT, sun karu da kashi 7 bisa 100 idan an kwatanta da makamancin lokacin bara wato daga adadin yuan biliyan 103.2 kwatankwacin dala biliyan 15.4. (Ahmad Fagam)