in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta gudanar da bikin baje kolin kayayyakin gini marasa gurbata muhalli a Chongqing
2019-04-07 15:44:21 cri
Daga ranar 10 zuwa 12 ga watan Mayu za'a gudanar da bikin baje-kolin kasa da kasa na kayayyakin gini marasa gurbata muhalli a yankin mulki na Chongqing dake kudu maso yammacin kasar Sin.

Bikin baje-kolin na kwanaki uku zai shafi bangarori masu yawa kama daga bangaren masu sarrafa kayayyakin kwalliyar gidaje, da na kawata dakuna, da kofofin daki, da tagogi da sauran bangarorin injuna.

Za a gudanar da bikin bake-kolin ne a cibiyar baje-kolin kasa da kasa dake Chongqing.

Baya ga batun nuna saurin bunkasuwa da yawan kwararru da za su ziyarci bikin, ana fatan bikin baje-kolin zai taimaka wajen bunkasa harkokin kasuwanci da hadin gwiwa tsakanin kamfanonin dake samar da kayayyakin gine-gine a yammacin kasar Sin.

Sama da masu baje-koli 1,000 da 'yan kallo dubu 50 ne ake sa ran za su halarci bikin baje-kolin inda ake sa ran yin ganawar masana'antu sama da 15. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China