in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An samu karuwar masu tafiye tafiye zuwa dazuwan kasar Sin a shekarar 2018
2019-03-17 16:00:44 cri
Wata kididdigar da mahukuntan kasar Sin suka fitar ta nuna cewa, yankunan dazukan kasar Sin sun kasance wasu muhimman wuraren da masu tafiye-tafiye don yawon shakatawa suka fi mayar da hankali, inda aka samu karuwar adadin wanda ya kai yuan trillion 1.5, kwatankwacin dala biliyan 224 a shekarar 2018.

Yawan tafiye-tafiyen zuwa dazuka ya karu zuwa biliyan 1.6 a shekarar da ta gabata, kamar yadda bayanan hukumar kula da gandun daji ta kasar Sin ta ayyana.

A bara, kasar Sin ta samar da wasu sabbin hanyoyi 10 a dazukan kasar, wanda shi ne kashin farko na irin wadannan hanyoyi.

Hukumar kula da filaye da gandun dajin kasar Sin ta fitar da wasu ka'idoji wadanda za su kyautata yanayin gandun daji, da nufin bunakasa al'amurran da suka shafi gandun dajin don ci gaban fannin yawon bude ido da kyautata yanayin muhallin halittu. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China