Jiya Laraba firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya shugabanci taron majalisar gudanarwar kasar, inda aka zartas da wasu daftarin dokoki domin taimakawa aiwatar da dokar zuba jari ta baki 'yan kasuwa, a kokarin kyautata yanayin kasuwanci. Yayin zaman an tsai da kudurin rage haraji kan kunshin kayayyaki da matafiya ke shigowa da su kasar, da kuma kayan da ake aikowa ta gidan waya, a wani mataki na fadada hada-hadar shigo da kayayyaki da kuma yin sayayya.
A yayin taron, an zartas da wasu daftarin gyararrun dokoki dangane da gudanar da mulki, tambari, gine-gine, siginar lantarki da dai sauransu, an kuma tsai da kudurin gabatar da su ga zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin don ya duba. An ba da shawarar cewa, za a tanadi "ka'idar rashin nuna bambanci" cikin dokar gudanar da mulki, kana kuma za a kara karfin hukunta wadanda suka keta hakkin yin amfani da tambari, tare da kara yawan kudin diyya.
Har ila yau, a yayin taron, an tabbatar da wasu matakan da za a dauka, domin ganin fararen hula sun kara cin gajiya ta fuskar ganin likita da shan magani. (Tasallah Yuan)