in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bangaren samar da kayayyaki na kasar Sin ya samu bunkasuwa a shekarar 2018
2019-03-25 09:47:00 cri
Sashen samar da kayayyaki na kasar Sin ya samu bunkasuwa a shekarar 2018, inda darajar samar da kayayyaki na bangaren ya karu da kashi 6.4 bisa 100 idan an kwatanta da makamancin lokacin bara wato ya zuwa yuan trillion 283.1 kwatankwacin dala trillion 42.3.

Adadin karuwar ya dan ragu da kasa da digo 0.2 daga shekarar 2017, kamar yadda hukumar kula da harkokin samar da kayayyaki da cinikayyar kasar Sin ta sanar.

Samar da kayayyakin bukatun yau da kullum ya karu da kashi 9.8 bisa 100 zuwa yuan trillion 13.3, wanda ya kai kashi 14.8 na ma'aunin tattalin arziki na GDP na bara. Adadin ya dan karu kadan idan an kwatanta da na shekarar da ta gabata.

Daga cikin adadin, bangaren sufuri ya karu da kashi 6.5 bisa 100, yayin da bangaren kulawa da adana kayayyaki ya karu da sama da kashi 13 bisa 100, hakan ya nuna cewa bangaren sufuri ya yi matukar samun tagomashi.

Adadin kudaden shigar da aka samu daga bangaren, ya karu da kashi 14.5 a shekarar da ta gabata zuwa yuan trillion 10.1, wato ya karu da kashi 3 inda ya haura na shekarar 2017.

An samu bunkasuwa a bangaren ne bisa hasashen manufar yanayin bunkasuwar tattalin arziki na kashi 6.6 na shekarar 2018, wanda ya zarta kashi 6.5 da aka yi hasashe tun da farko. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China