Wani jami'in hukumar ya bayyanawa kamfanin dillancin labaru na Xinhua cewa, an yi musayar wuta ne a ranar 2 ga wata, bayan kungiyar 'yan banga ta yankin Kaura Namoda dake jihar Zanfara ta samu labari cewa, akwai wasu tsageru da suka taru a dajin dake dab da yankin. Daga baya kungiyar ta tura wasu membobinta da kuma wasu jama'a zuwa wurin, inda suka yi musayar wuta.
A wannan rana kuma, shugaban majalisar dokokin jihar Zanfara Sanusi Rikiji ya yi kira ga kungiyar 'yan banga da ta taimakawa ga hukumar tsaron ta farin kaya, domin kada a dauki matakan murkushe tsagerun daga bangare daya ba. (Zainab)