Kwamishinan lafiya na jihar Legas, Jide Idris ya shaidawa manema labarai cewa, an tabbatar da mutuwar mutane 18 kana an ceto sama da mutane 60.
Ya ce, koda yake an kawo karshen aikin ceto da ake yi, amma ana iya ganin ma'aikatan lafiya suna kokarin taimakawa wadanda lamarin ya shafa.
A cewar jami'in, zai yi wahala a halin yanzu a bayyana yawan wadanda lamarin ya shafa a hukumance , ganin yadda ake ci gaba da tattara alkaluman wadanda suka mutu da wadanda suka jikkata.
Yanzu haka dai, akwai a kalla manyan asibitoci uku da wani asibitin kula da kananan yara guda a Legas dake jinyar wadanda hadari ya shafa
Mai magana da yawun babban sakataren MDD Stephane Dujarric, ya shaidawa taron manema labarai cewa, Antonio Guterres ya kadu matuka da hadarin rubtawar ginin da ya faru a Najeriya, yana mai cewa, jami'in na MDD zai aikawa gwamnatin Najeriya sakonsa na ta'aziyya dangane da faruwar wannan iftila'i.(Ibrahim)