in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta bada rahoton karuwar rikice-rikice da mace-mace a iyakar Niger da Nijeriya
2019-04-06 15:22:30 cri

Ofishin kula da harkokin jin kai na MDD, ya bada rahoton karuwar rikice-rikice da daidaitar mutane a cikin watan Maris, a kan iyakar Niger da Nijeriya, inda ake kai hare-hare kan fararen hula da jami'an tsaro, lamarin da ya yi sanadin mutuwar fararen hula 88.

Mataimakin Kakakin ofishin Jens Laerke, ya bayyana cewa, an samu karuwar rikice-rikicen ne a yankin Diffa dake kudu maso gabashin Niger wanda ke iyaka da Nijeriya da Chadi.

Ya ce a watan Maris kadai, fararen hula 88 aka kashe, adadin da ya yi yawa sosai idan aka kwatanta da 107 da aka kashe a shekarar 2018.

Rikice-rikicen na da alaka da karuwar ayyukan kungiyoyi masu dauke da makamai, musammam Boko haram, dake kai hare-hare yankin tafkin Chadi.

A cewar MDD, kungiyar na barazana sosai ga tsaro da ayyukan jin kai da harkokin shugabanci a yankin.

Jens Laerke ya ce jami'an bada agaji dake Niger sun damu da yadda kungiyoyi masu dauke da makamai suka dauki sabon salon kai hare-hare kan mutane mafi rauni a yankin, ciki har da wadanda suka rasa matsugunansu da 'yan gudun hijira. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China