Wata sanarwa da ma'aikatar ta fitar, ta ce Mr. Li zai gudanar da ziyarar ne tsakanin ranekun 8 zuwa 12 ga watan Afirilun nan, zai kuma ziyarci birnin Brussels domin halartar taron jagororin Sin da Turai na tattauna makomar sannan a karni na 21.
Kaza lika zai kai ziyarar aiki kasar Croatia, tare da ganawa da shugabannin tsakiya da gabashin Turai na CEEC.
Wannan ce dai ziyarar farko da firaminista Li zai gudanar a ketare cikin wannan shekara, tun bayan ziyarar da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gudanar a kasashen Italiya, da Monaco da kasar Faransa a watan jiya.(Saminu Alhassan)