in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Manoma daga Asiya da Afirka fiye da miliyan 1 sun ci gajiyar ingantacciyar shinkafar "GSR" ta kasar Sin
2019-04-04 11:07:39 cri

Masana kimiyyar aikin gona na kasar Sin, sun samar da wasu sabbin nau'ikan irin shinkafa masu inganci da ake kira "Green Super Rice ko GSR" a takaice, ga kasashe masu tasowa na Asiya da Afrika, domin rage yunwa da karawa manoma kudin shiga.

Aikin da aka kaddamar tun shekarar 2008, bisa goyon bayan Gwamnatin kasar Sin da Gidauniyar Mill and Melinda Gates, wanda ya samar da nau'ikan irin shinkafa 78 da aka noma a gonaki masu fadin kadada miliyan 6.12 a kasashe 18, ana fatan zai amfani kananan manoman shinkafa miliyan 30 a nahiyoyin Asia da Afrika.

Nau'ikan irin shinkafar GSR, ingantattu ne da za su iya samar da amfanin gona mai yawa sosai. Sannan ba sa bukatar takin zamani, da maganin kashe kwari da ruwa mai yawa, domin suna iya jure kwari, da cututtuka, da fari, da sauran wasu abubuwa masu barazana ga noman shinkafa.

Inda ake sa ran amfani da su sun hada da kasashe 9 na nahiyar Asiya, da wasu 9 na nahiyar Afrika, da suka hada da Mozambique, da Tanzania, da Rwanda, da Liberia, da Habasha, da Uganda, da Nigeria, da Mali da kuma Senegal.

Yanzu haka dai ana sa aya ga aikin samar da wasu sabbin nau'ikan shinkafa masu inganci da ake kira GSR a takaice. Amma kasashen Afirka da suka ci gajiyar shinkafar, a shirye suke wajen inganta hadin kai da kasar Sin. Ishaq Mohammed, shehun malami daga cibiyar nazarin hatsi ta Nigeria ya ce, yanzu kamfanonin iri fiye da 20 na Nigeria sun fara amfani da shinkafar GSR, wadanda suke kokarin yin amfani da gonaki yadda ya kamata, da kuma samar da shinkafa mai yawa. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China