Bisa wannan shirin da aka gabatar, za a gina cibiyoyin ne bisa tushen wasu tsoffin cibiyoyin jigilar kaya da ake da su yanzu, musamman ma wadanda ke mallakar kayayyakin more rayuwa masu inganci, da samun dimbin aikace-aikacen kasuwanci, da taimakawa raya yankunan da cibiyoyin suke ciki, gami da samar da tasiri kan wasu sana'o'i.
A shekarar da muke ciki, hukumomin kasar Sin za su tabbatar da jerin sunayen wurare kimanin 15 da za a gina wadannan sabbin cibiyoyin zirga-zirgar kayayyaki, tare da la'akari da bukatun da ake da su, a kokarin gudanar da wasu manyan tsare-tsaren kasar, irinsu shawarar "Ziri Daya da Hanya Daya", da shirin raya yankunan Beijing-Tianjin-Hebei, da shirin raya wani yanki mai ci gaban tattalin arziki dake dab da kogin Yangtse, da shirin raya yankin mashigin teku na Guangdong-Hong Kong-Macao, da shirin dunkulewar garuruwan dake yankin delta din kogin Yangtse, da dai makamantansu. (Bello Wang)