Wata sanarwa da rukunin kamfanin ya fitar, ta bayyana cewa, wata tawagar kasar karkashin jagorancin hukumar binciken hadurra (AIB) ta tashi zuwa Paris na kasar Faransa dauke da na'urar nadar bayanai(FDR) da na'urar dake nadar muryar matukin jirgin(CVR) domin gudanar da bincike.
An yanke shawarar aika na'urorin nadar bayanai da ta muryar zuwa Faransa ne,kwana guda bayan da shugaban kamfanin jiragen saman kasar ta Habasha, Tewolde Gebremariam, ya bayyana cewa, kasar dake gabashin Afirka, ba ta da kayayyakin aikin da ake bukata na binciken wadannan na'urori.
A ranar Laraba ce dai, Gebremariam ya bayyana cewa, za a aika wadannan na'urorin zuwa kasar waje don fara gudanar da bincike a kansu.(Ibrahim)