in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An gano akwatunan ajiye bayanan jirgin saman Habasha da ya fadi
2019-03-12 10:15:46 cri

Kamfanin zirga-zirgar jiragen sama na kasar Habasha Ethiopian Airlines ya sanar a jiya Litinin da cewa, masu aikin ceto sun gano akwatuna guda 2 masu ajiyar bayanan jirgin saman da ya gamu da hatsari, wato wadanda ke daukar alkaluma masu alaka da yadda jirgi ke shawagi, da mai daukar muryar matukan jirgin.

A ranar Lahadin da ta gabata ne, jirgin kamfanin Ethiopian Airlines ya tashi daga Addis Ababa dake Habasha da niyyar zuwa Nairobi na kasar Kenya. Sai dai jirgin ya fadi mintuna kadan bayan tashinsa, lamarin da ya yi sanadin mutuwar dukkan fasinjoji da ma'aikata 157 dake ciki baki daya, ciki har da wasu Sinawa 8.

Bayan abkuwar lamarin, kamfanin Ethiopian Airlines ya dakatar da amfani da dukkan jiragen samansa masu samfuri iri daya da wanda ya gamu da hatsari, wato samfurin Boeing 737 MAX 8. Kuma zuwa yanzu, ba a tabbatar da lokacin sake fara amfani da jiragen ba. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China