Bisa labarin da kafofin watsa labaru na kasar suka bayar, hadarin ya haddasa mutuwar mutane a kalla 20 tare da raunatar mutane 43, wasu daga cikinsu sun ji rauni mai tsanani.
Bayan abkuwar hadarin, shugaban kasar Masar Abdel Fattah al Sisi ya bayyana cewa, za a yanke hukunci kan wadanda suka haddasa hadarin, kana ya nuna alhini ga mutanen da suka mutu a sakamakon hadarin. Ministan harkokin sufuri na kasar Hesham Arafat ya yi murabus a wannan rana domin wannan lamari, firaministan kasar Mostafa Madbouly ya amince da takardar yin murabus din sa.
Majalisar ministocin kasar ta amince da samar da kudi ga iyalan mutanen da suka mutu da kuma mutanen da suka ji rauni a sakamakon hadarin. (Zainab)