in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU da NATO sun yi kira game da kara azama wajen aiwatar da tsarin tawagar tsaron Afirka
2019-04-04 09:54:51 cri
Kungiyar hadin kan Afirka ta AU, da kungiyar tsaro ta NATO, sun yi kira game da bukatar kara azama, wajen aiwatar da tsarin tawagar ko ta kwana ta tsaron Afirka.

Kungiyoyin biyu, sun yi fatan dukkanin sassa na masu ruwa da tsaki, za su yi hadin gwiwa wajen ganin ayyukan tawagar mai lakabin ASF sun kankama yadda ya kamata.

Wata sanarwa da kungiyar AU ta fitar a jiya Laraba, ta ce wakilan kungiyoyin biyu sun gabatar da wannan kira ne, bayan taron kwamishiniyar AU mai kula da harkokin kwadago kimiyya da fasaha Sarah Anyang Agbor, da kwamandan tawagar hadin gwiwa ta aikin soja karkashin NATO mai sansani a Italiya, da kwamandan sojojin ruwan Amurka mai lura da Turai da Afirka Admiral James G. Foggo III.

Taron jami'an wanda ya gudana a birnin Addis Ababan kasar Habasha, ya amince da muhimmancin kara hada karfi da karfe, tsakanin AU da NATO a fannonin da suka jibanci siyasa, da samar da horo, da hadin gwiwar nahiyoyi.

Da take tsokaci yayin taron, kwamishiniyar AU Sarah Anyang Agbor, ta yi karin haske game da wasu ayyuka da AUn ta tsara aiwatarwa, ciki hadda "shirin dakatar da bude wuta nan da shekarar 2020", wanda kungiyar ta ce ya haifar da kyakkyawan sakamako a fannin dakile tashe tashen hankula, da kandagarkin aukuwar su, tare da sake ginin wuraren da yake yake suka daidaita.

Ana sa ran tawagar ASF za ta gudanar da ayyuka daban daban a sassan nahiyar Afirka, wadanda suka hada da wanzar da zaman lafiya karkashin rundunar soji, da aikin sintiri mai kunshe da 'yan sanda da fararen hula, karkashin jagorancin kungiyar AU. Kaza lika za a rika tura tawagar ayyuka a duk lokacin da bukatar hakan ta taso a sassan kasashen nahiyar mambobin kungiyar AUn su 55. (Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China