in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Adadin wadanda suka mutu sanadiyyar mahaukaciyar guguwar Idai a Zimbabwe ya karu zuwa 268
2019-04-03 11:27:28 cri
Ministar yada labarai ta kasar Zimbabwe dake yankin kudancin Afrika, Monica Mutsvangwa, ta ce adadin wadanda suka mutu a kasar sanadiyyar mahaukaciyar guguwar Idai ya karu zuwa 268.

Monica Mutsvangwa ta bayyana yayin wani taron manema labarai cewa, abun bakin ciki ne yadda adadin mutanen da suka mutu ya kai 268, kuma har yanzu ana tsammanin karuwarsa yayin da ake ci gaba da aikin bincike.

Ministan kananan hukumomi da ayyukan gwamnati da samar da gidaje na kasar, July Moyo, wanda kuma ke jagorantar aikin binciken, ya ce adadin wadanda suka mutun ya hada da gawarwakin da aka samu rahoton an gansu a saman ruwa a makwabiciyar kasar Mozambique da kuma wadanda aka binne a Zimbabwen. Ya ce gwamnati za ta ci gaba da aikin bincike da ceto. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China