Gwamnatin kasar ta bayyana cewa, an samu ceto karin mutane a Beira dake lardin Sofala na tsakiyar kasar, wanda ya sanya adadin wadanda aka ceto kaiwa ga mutum 128,941.
Yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a yau, ministan ma'aikatar filaye, muhalli da raya karkarar kasar Celso Correia, ya ce adadin wadanda suka rasa rayukan su sakamakon ibtila'in ya kai mutum 446.
A dai wannan rana ne kuma, jami'an ba da agajin jin kai na kasar Sin su 65 suka isa filin jiragen sama na Beira, tare da kayan aikin jin kai da nauyin su ya kai tan 20, ciki hadda kayan jiyya, da na aikin zakulo wadanda ibtila'in ya rutsa da su, da kuma kayan sadarwa. (Saminu)