Babban daraktan kungiyar Roberto Azevedo, ya ce idan aka yi duba da yadda ake fuskantar matsi a fannonin cinikayya, rage hasashen da aka yi ba zai zamo wani abun mamaki ba. Roberto Azevedo ya bayyana hakan ne yayin fitar da wani rahoto, game da alkaluman kididdigar cinikayya na kungiyar.
Alkaluman na baya bayan nan a cewar sa, alamu ne na raguwar alkaluman tattalin arziki ko GDPn wasu kasashe, wadanda suka hada da yankunan Arewacin Amurka, da Turai, da wasu sassa na nahiyar Asiya.
Rahoton ya kara da cewa, karin dalilai da suka haifar da hasashen koma bayan, sun hada da karewar tasirin manufar Amurka ta fadada kashe kudade, da kammala wasu manufofin shigar da karin kudade cikin harkokin tattalin arziki a nahiyar Turai, da kuma karkata alakar da kasar Sin ta yi daga samar da karin hajoji da zuba jari, zuwa ga fannin ayyukan ba da hidima, da kyautata amfani da hajoji a cikin gida. (Saminu)