in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ghana na fama da karancin lantarki
2019-04-03 09:15:09 cri
Al'ummun kasar Ghana na fama da karancin wutar lantarki, sakamakon rufe cibiyar sarrafa iskar gas da ake amfani da ita wajen samar da lantarkin.

Ma'aikatar makamashi ta kasar ta ce rufe cibiyar mai nisan kilomita 329 yamma da birnin Accra, ya biyo bayan kokarin da ake yi ne na hade bututan ta, da na kamfanin iskar gas na yammacin Afirka.

Da ma dai 'yan kasar Ghana sun fuskanci karancin lantarki mai tsanani a farkon shekarun 2013 da 2015. To sai dai a wannan karo, mataimakin minista a ma'aikatar makamashin kasar William Owuraku Aidoo ya ce, burin su shi ne rage tasirin aikin da ake yi a yanzu, duba da yadda lamarin ke haifar da wahalhalu ga al'umma, da ma tarin kalubale ga masu sana'oi. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China