in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU, SCO sun sanya hannu kan yarjejeniyar yaki da ta'addanci
2018-12-12 09:57:27 cri
A jiya Talata ne, sassan yaki da ta'addanci na kungiyoyin tarayyar Afirka (AU) da ta hadin gwiwa ta Shanghai (SCO) suka sanya hannu kan alakar fahimtar juna (MOC) game da yaki da ta'addanci.

Darektan cibiyar nazari da binciken ayyukan ta'addanci ta kungiyar tarayyar Afirka (ACSRT) Larry Gbevlo-Lartey da shugaban sashen yaki da ayyukan ta'addanci na kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai (SCO RATS) Yevgeniy Sergeyevich Sysoyev ne suka sanya hannu kan wannan yarjejeniya bayan kwashe shekaru biyu suna tattaunawa.

Yarjejeniyar dai za ta baiwa sassan biyu damar yin hadin gwiwa ta hanyar musayar kwarewa da yin atisaye a fannin yaki da ayyukan ta'addanci.

Kamfanin dillancin labarai na kasar Aljeriya APS ya ruwaito Gbevlo-Lartey na cewa, cibiyar nazari da binciken ayyukan ta'addanci ta kungiyar tarayyar Afirka (ACSRT) wani muhimmin tsari ne na hukumar gudanarwar kungiyar, don haka akwai bukatar a kara hada kai da sauran hukumomi ta yadda za a kara gano hanyoyin da suka dace na inganta hadin gwiwa.

A nasa jawabin Sysoyev, ya bayyana cewa, yarjejeniyar za ta baiwa sassan biyu damar yin musayar kwarewa da atisaye kan yadda za a yaki ayyukan ta'addanci, da ma hanyoyin da suka dace na magance barazanar ta'addanci. (Ibrahim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China