in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shafin Taobao na sayayya kai tsaye na samun babban tagomashi
2019-04-01 12:02:36 cri

Kamfanin Taobao, daya daga manyan shagunan sayayya ta yanar gizo mallakar gungun kamfanonin Alibaba, ya yi hasashen samun karin miliyoyin abokan hulda.

Daya daga manyan daraktocin kamfanin na Taobao Wen Zhong, ya ce cikin shekaru 3 da suka gabata kamfanin ya samu manyan nasarori, inda shafin sa na sayar da kaya kai tsaye ko "Taobao Live" ya zamo abun zabi ga kowa, musamman a fannin hada hadar sayayya kai tsaye ta shafukan kamfanin.

A bara darajar jarin kamfanin karkashin shafin "Taobao Live" ta kai yuan biliyan 100, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 14.93, inda yake samun karuwar ci gaba ta kusan ninki hudu a duk shekara. Kana ya zuwa yanzu, ana tallata nau'o'in kayayyaki da yawansu ya kai 600,000 a kan shafin.

Shafin "Taobao Live" ya samar da ayyukan yi ga manoma, da 'yan kasuwa, da sauran masu sana'o'in hannu, ta yadda suke iya tallata hajojin su kai tsaye, su kuma tattauna tare da masu bukatar sayayya.

A wannan shekara ta bana, Taobao na hasashen shaguna kusan 200 dake tallata hajojin su a shafin sa, za su fara amfani da shafin na hada hada kai tsaye, wanda hakan ka iya kai darajar yawan cinikayyar da kowane dayan su zai yi, zuwa kudi sama da yuan miliyan 100. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China