in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An gudanar da shawarwarin harkokin tattalin arziki da cinikayya karo na 8 tsakanin Sin da Amurka
2019-03-30 15:56:47 cri
An gudanar da shawarwarin harkokin tattalin arziki da cinikayya zagaye na takwas, tsakanin Sin da Amurka a nan birnin Beijing, daga ranar 28 zuwa 29 ga wata. shawarwarin sun gudana ne karkashin jagorancin mataimakin firaministan kasar Sin Liu He, wanda kuma shi ne jagoran shawarwarin daga bangaren Sin, da kuma wakilin kasar Amurka kan harkokin cinikayya kana ministan kudin kasar, Steven Mnuchin, inda bangarorin biyu suka tattauna kan takardun yarjejeniyar da ake neman cimmawa, tare kuma da samun sabon ci gaba.

Bisa goron gayyatar da aka ba shi, Mr. Liu He, mataimakin firaministan kasar Sin zai kai ziyara kasar Amurka a sati mai zuwa, inda zai halarci shawarwarin da za a gudanar a zagaye na tara a birnin Washington D.C.(Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China