Jami'in ya ce, an gayyaci wakilin Amurka a fannin cinikayya Robert Lighthizer da sakataren baitul-malin Amurka Steven Mnuchin zuwa kasar Sin don wannan tattaunawa.
A bangare daya kuma, shi ma mataimakin firaministan kasar Sin Liu He, mamban hukumar siyasa na kwamitin koli na JKS kana jagoran bangaren kasar Sin a tattaunawar cinikayya da tattalin arziki tsakanin Sin da Amurka an gayyace shi zuwa Washington D.C. don halartar zagaye na 9 na tattaunawar sassan biyu da aka shirya yi a farkon watan Afrilun wannan shekara.
A baya-bayan nan, sassan biyu sun sha yin tattaunawa ta wayar tarho kan batutuwan da suka shafi tattalin arziki da cinikayya, inda suka amince su gudanar da zagaye na 8 da na 9 na tattaunawa tsakanin manyan jami'an kasashen biyu. (Ibrahim)