Shugaban sashen kula da ayyukan bada hidimomin cinikayya na ma'aikatar kasuwancin Sin ya bayyana a jiya Talata cewa, Jimillar kudaden shigi da fici da Sin ta samu a fannin aikin bada hidima a bara ya zarce Yuan biliyan 5240, wanda ya kai na koli a tarihi. Saurin karuwar jimillar da kasar Sin ta samu ya wuce sauran manyan kasashe da yankuna masu karfin tattalin arziki, kuma jimillar tasa Sin ta ci gaba da zama ta biyu a wannan fanni a duniya baki daya. (Kande Gao)