Chu Shijia wanda ya bayyana hakan yayin taron manema labarai, ya ce yadda tattalin arzikin duniya ke ci gaba da farfadowa sannu a hankali, da matakan kasar Sin na bude kofa da manufofin raya harkokin cinikayya, da yadda ake farfado da masana'antu da matakan inganta hukumomin da abin ya shafa, za su karawa harkokin cinikayyar kasar ta Sin karfi a wannan shekara.
Ya kuma bayyana cewa, ciniyayyar kayayyaki a watan Janairu ya kara daga matsayin ci gaban.
A shekarar da ta gabata, kasar Sin ta sayar da kayayyakin da darajarsu ta kai dala triliyan 4.62, karuwar kaso 12.6 kan na shekarar da ta gabace ta, adadin da ya dara na manyan kasashe kamar Amurka da Jamus da Japan da ma matsakaicin adadin manyan kasashe masu karfin tattalin arziki.(Ibrahim)