Taron na yini 5, ya samu halartar kimanin mutane 400, da suka kunshi kwararru, da jami'an gwamnati, da masu tsara manufofi, da sauran sassan masu ruwa da tsaki, musamman daga yankunan gabashi da arewacin nahiyar Afirka da ma sauran yankuna.
Ana dai sa ran mahalarta taron za su yi musayar ra'ayoyi, game da hanyoyin magance karancin ruwa da abinci, da batun inganta dabarun kare filaye daga kwararar hamada, da lalacewar kasa sakamakon fari da sauyin yanayi. Kaza lika za a tattauna game da sauran al'amura masu nasaba da kyautata rayuwar daukacin bil Adama.
Da yake tsokaci game da hakan, mataimakin darakta, kuma wakilin yankunan gabashi da arewacin Afirka a taron Abdessalam Ould Ahmed ya jaddada cewa, za a tattauna bukatun gaggawa na yankunan a 'yan kwanaki masu zuwa, musamman duba da yadda suke da tasiri wajen dakile ci gaban tattalin arziki, da yada talauci. Za kuma a tattauna game da batun karancin guraben ayyukan yi, da batun masu ci rani, lamurran da har kullum, ke yin tarnaki ga zaman lafiya da daidaito a yankunan. (Saminu)