A cewar kakakin shugaban hukumar Ravina Shamdasani, mummunan harin da aka kai ranar Asabar, ya kara yawan kashe-kashen da ake yi a yankin Mopti, wanda ya samo asali daga rikici tsakanin al'ummomi, da kuma wasu kungiyoyin masu ikirarin kare kansu, dake kokarin fatattakar kungiyoyin masu tsattsauran ra'ayi.
Yayin wani taron manema labarai, Ravina Shamdasani ta ce harin da aka kai Ogossagou na yankin Mopti dake tsakiyar Mali, shi ne na baya-bayan nan cikin jerin hare-hare da rikice-rikice dake faruwa a yankin.
Ta ce daga watan Maris na 2018 zuwa yanzu, wadannan rikice-rikice sun yi sanadin mutuwar mutane 600 da suka hada da mata da maza da yara, yayin da wasu dubbai suka rasa matsugunansu, a yankin Mopti kadai. ((Fa'iza Mustapha)