in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sakataren MDD ya yi kira da a kawo karshen nuna wariyar launin fata
2019-03-26 09:16:07 cri
Babban sakataren MDD Antonio Guterres ya bukaci al'ummomin kasashen duniya da su sake jaddada alkawuran da suka yi na kawo karshen nuna wariyar launin fata.

Guterres ya bayyana hakan ne yayin bikin ranar yaki da nuna wariyar launin fata ta kasa da kasa. Yana mai cewa, lokaci ya yi "da za mu sabunta alkawuran da muka yi don kawo karshen nuna kabilanci, da wariyar launin fata, kyama da dangoginsu, ciki har da nuna bambancin matsayi, da yare, da kyamar da ake nunawa musulmi da sauransu.

Ya ce, harin da aka kai wasu masallatai biyu a New Zealand makonnin biyu da suka gabata, suna daga cikin abin takaici na baya-bayan nan dake haddasa irin wannan matsala. Kuma a duk lokacin da aka kaiwa jama'a hari a zahiri, ko ta fatar baka ko ta kafar watsa labarai, saboda kabilarsu , addini ko yarensu, to an taba al'umma baki daya. Jami'in na MDD ya kara da cewa, lokaci ya yi da dukkanmu za mu tashi tsaye mu kuma kare manufofin da suka shafi daidaito da mutuncin dan-Adam.

Guterres ya kuma bukaci mai ba shi shawara na musamman a fannin riga kafin aukuwar kisan kiyashi, da ya tattara tsarin MDD ta yadda za a fito da dabaru da matakan da suka dace na kawo karshen kalaman nuna kyama. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China