in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babban jami'in MDD yayi kiran a bullo da ingantaccen tsari a taron kolin MDD kan sauyin yanayi
2019-03-29 10:38:37 cri

Sakataren janar na MDD Antonio Guterres, ya bukaci shugabannin kasashen duniya dasu halarci taron New York a watan Satumba kuma su gabatar da muhimman tsare tsaren da zasu taimaka wajen dakile dumamar yanayi a lokacin taron kolin MDDr kan batun sauyin yanayi.

Guterres shi da kansa ya kira taron kolin, wanda za'a gudanar a ranar 23 ga watan Satumba, kwana guda gabanin fara babban taron shekara na makon MDD, domin nazartar yadda za'a tinkari batun sauyin yanayi a duniya.

"Yana da matukar muhimmanci mu warware matsalar sauyin yanayi ta hanyar sanya babban buri. Ina fadawa shugabannin duniya cewa: kada kuce zaku zo don ku gabatar da jawabai, sai dai ku zo da wasu muhimman shirye shirye," Guterres ya bayyana hakan ne ga taron manema labaru a lokacin gabatar da rahoton shekara na duniya na hukumar hasashen ruwan sama ta duniya (WMO).

Hakan yana nufin za'a tabbatar da bada cikakkiyar gudunmowa karkashin yarjejeniyar sauyin yanayi ta Paris nan da shekarar 2020 da kuma nunawa duniya yadda za'a rage dumamar yanayin duniya da kashi 45 bisa 100 nan da shekaru 10 masu zuwa da rage dumamar yanayin da kasa da maki guda a duniya nan da shekarar 2050, inji mista Guterres.

Idan har ba'a dauki wannan mataki ba, batun dumamar yanayin duniya zai kasance mai wahalar gaske, inji shi. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China