Manufar kudirin mai lamba 2462 da kasar Faransa ta gabatar, ita ce, sabunta kudurori da ake da su a baya, sannan a kuma yi amfani da su cikin sabbin hanyoyin da 'yan ta'adda ke samun kudadensu da ma sabbin kalubalen da ake fuskanta a wannan fanni.
Kudurin ya nuna damuwa cewa, 'yan ta'adda za su iya yin amfani da harkokin kasuwanci na halal da kungiyoyi masu zaman kansu ta hanyoyi da ba su dace ba, su kuma yi amfani da hanyoyin biyan kudade na zamani, kamar katunan banki da tsarin biyan kudi ta wayar salula ko wasu kadarori.
Bugu da kari, kudurin ya bayyana damuwa, kan yadda 'yan ta'adda da masu goya musu baya ke ci gaba da amfani da bayanai da fasahohin sadarwa na zamani, musamman, intanet, wajen kaddamar da ayyukan ta'addanci, da tunzura jama'a da daukar sabbin mambobi, da samar da kudade ko tsara kai hare-hare na ta'addanci.
Don haka, kudirin ya yi kira ga dukkan kasashe, da su kara kokarin sanya ido da gudanar da hada-hadar kudade bisa doka, ciki har da tantance da magance barazana dake da nasaba da kadarori yadda ya kamata, da barazanar sabbin hanyoyi hada-hadar kudi, da ma hanyoyin hada-hadar kudi da jama'a ke ribibi.(Ibrahim)