in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Zambia na hada hannu da shugabannin kasashen yankin kudancin Afrika don magnace hare-haren kyamar baki a Afrika ta kudu
2019-04-01 09:39:21 cri
Shugaban kasar Zambia Edgar Lungu, ya yi kira ga takwarorinsa na yankin kudancin Afrika, da su hada hannu wajen magance sabbin hare-haren kyamar baki da suka kunno kai a Afrika ta kudu.

Wani sabon harin kyamar baki ya barke a Afrika ta kudu, inda ake kai hari kan gidaje da fasa shagunan baki 'yan wasu kasashen Afrika dake kasar.

Sanarwar da kakakin fadar shugaban kasar Zambia Amon Chanda ya fitar, ta ruwaito cewa, shugaban kasar ya damu da hare-haren da ake kai wa baki a kasar Afrika ta kudu.

Edgar Lungu wanda shi ne shugaban kungiyar raya yankin kudancin Afrika ta SADC, wadda ayyukanta ke mayar da hankali kan harkokin siyasa da tsaro, ya tuntubi shugaban kasar Namibia Hage Geingob, wanda shi ma shugaban kungiyar SADC ne, da kuma shugaban Afrika ta kudu Cyril Ramaphosa, domin taimakawa Afrika ta kudun magance mummunar dabi'ar a yankin.

Sanarwar ta kuma ce Shugaban na Zambia, ya kuma bayyana rashin jin dadi game da matakin ramuwar gayya da Malawi ta dauka. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China