in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi ya gabatar da muhimman shawarwari 3 da za su kyautata dangantakar Sin da Jamus
2019-03-27 10:25:27 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel a ranar Talata a birnin Paris, inda ya gabatar da wasu muhimman shawarwari 3 wadanda za su kara kyautata dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.

Da farko, ya kamata kasashen biyu su zurfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu domin buga misali ga hadin gwiwar cin moriyar juna.

Na biyu, ya kamata kasashen biyu su kasance manyan jagorori game da dangantakar Sin da EU tare kuma da tabbatar da zaman lafiyar duniya.

Na uku, kasashen biyu su kara daga matsayin hadin gwiwarsu wajen tafiyar da harkokin kasa da kasa da kuma kare manufar cudanyar kasa da kasa.

Merkel ta ce, gwamnatin Jamus tana son kara zurfafa mu'amalar tattalin arziki da cinikayya da kasar Sin a sabon zamani, kuma a shirye take ta shiga taron dandalin hadin gwiwar shawarar ziri daya da hanya daya a zagaye na biyu.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China