Xi Jinping ya ce, ya kamata bangarori daban daban su tabbatar da adalci don warware matsalar tafiyar da harkokin duniya, da yin shawarwari da fahimtar juna don warware matsalar rashin yin imani da juna, da yin kokari da hadin gwiwa don tabbatar da zaman lafiya, da kuma samun moriyar juna don warware matsalar samun ci gaba.
Xi Jinping ya kara da cewa, an inganta tunanin hadin gwiwar tattalin arziki a tsakanin kasa da kasa da tsarin gudanar da cinikayya tsakanin bangarori daban daban ta hanyar raya shawarar "ziri daya da hanya daya", kana Sin ta yi maraba da kasa da kasa ciki har da kasar Faransa da su shiga shirin raya shawarar "ziri daya da hanya daya". Ya kamata Sin da Turai su sa kaimi ga yin shawarwarin cimma yarjejeniyar zuba jari a tsakaninsu. (Zainab)