in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a sake bude hanyar zirga-zirgar jiragen ruwa tsakanin Masar da Saudiya
2019-02-22 10:35:22 cri
Jami'in kula da tashoshin jiragen ruwa dake bakin tekun Bahar Maliya na kasar Masar, Aymn Salih, ya sanar a jiya Alhamis cewa, za a sake bude hanyar zirga-zirgar jiragen ruwa da ta hada Port Tewfik na kasar Masar da Jeddah na kasar Saudiya.

An datse hanyar zirga-zirgar jiragen ruwan ne a shekarar 2006, bayan wani babban jirgin ruwa mai taken "Salam 98" ya nutse cikin Bahar Maliya, tare da haddasa asarar rayuka fiye da 1000. An ce, sake bude hanyar za ta samar da dimbin guraben ayyukan yi, gami da saukaka aikin ciniki. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China