Hukumar gudanarwar al'adu da yawon bude ido ta Shanghai ta sanar cewa, kasashen Morocco, Madagascar, Papua New Guinea, Gabon da Turkmenistan zasu halarci bikin na wannan karon.
Bikin na shekara shekara wani dandali ne dake bajekolin kayayyakin gargajiyar kasar Sin, a yayin da hukumomin dake kula da yawon shakatawa na kasa da kasa suke bajekolin irin albarkatun da suke dasu tare da manyan fasahohinsu a lokacin bikin.
Taron bajekolin zai hallara cibiyoyi da hukumomin yawon bude ido na cikin gida, da masu tafiyar da aikin yawon bude ido ta intanet, da kamfanonin jiragen sama, da masu kula da lambunan shakatawa, da otel otel da kamfanonin inshora. Ana saran bikin zai janyo hankalin sama da kwararrun masu ziyara 15,000, da masu sha'awar tafiye tafiye 50,000 a wannan shekarar, inji mashirya taron.
A shekarar 2018, Sinawa masu sha'awar yawon shakatawa sun yi tafiye tafiye kasashen waje kimanin miliyan 150, da kuma tafiye tafiye a cikin gida kimanin biliyan 5.5. Muhimman wuraren yawon shakatawa na babban yankin kasar Sin ya samu baki 'yan yawon shakatawa kimanin miliyan 48 a shekarar bara. (Ahmad)