A yayin wani taron manema labarai da ya gudana a jiya Laraba, gwamnatin ta ce ya zuwa yanzu, kamfanonin ketare dake da hedkwatocinsu a birnin Shanghai sun kai 580, yayin da cibiyoyin nazari da kirkire-kirkire masu jarin waje suka kai 411 a birnin.
Baya ga haka, kamfanonin birnin, sun zuba jari tare da gudanar da harkokinsu a kasashe da yankuna 178 na duniya, kuma yawan jarin da yankin gwajin ciniki maras shinge ya zuba a ketare, ya dauki kashi 70 cikin dari na gaba dayan jarin da birnin ya zuba. (Lubabatu)